Kyakykyawan Jagorancin Ganduje ne yasa ya zama Gwarzon Gwamnan Shekara ta 2021- Dr. Gawuna

Date:

Daga Khalifa Abdullahi
 Mataimakin gwamnan jihar Kano Dr.Nasiru Yusuf Gawuna ya taya shugaban sa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje murnar samun lambar yabo ta “Gwarzon Gwamnan Shekara ta 2021” Wanda jaridar Sun ta bashi a Jiya a sabar  .
 Mataimakin Gwamna ya ce …. “Gwamna Ganduje dan kishin Jihar Kano ne Kuma gogagge ɗan siyasa wanda muke alfahari da shi, Saboda Kyakkyawan salon jagoranci da gudummawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Kano”.
Cikin Wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Mataimakin Gwamna Hassan Musa Fagge ya aikowa Kadaura24 yace Dr. Gawuna yace  Ganduje ya cancanci kyautar da aka bashi, idan aka yi la’akari da yadda a cikin shekaru 6 da suka gabata ya gudanar da aiyukan da Suka daga daraja da kimar kano a idanun Duniya ta fuskar aiyukan ci gaba
 “Wannan lambar yabo da Jaridar kasa ta baka ta tabbatar da cewa ana lura da nasarorin da kake samu”. Inji Gawuna
 Ina so in yi kira ga mutanen Kano da su ci gaba da ba da goyan baya tare da ba da haɗin kai ga kyawawan manufofi da Tsare-tsaren gwamnatin waɗanda suka kawo canji Mai ma’ana.
 Har wa yau ina taya Mai Girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje murnar wannan kyautar da zata kara masa kwarin gwiwar yi wa Jihar Kano aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...