Matawalle ne jagoran APC a Zamfara- MaiMala Buni

Date:

Shugaban riƙo na jam’iyyar APC ta ƙasa kuma gwamnan jihar Yobe Maimala Buni ya ce daga yau Gwamna Bello Matawalle ne jagoran jam’iyyar a jihar Zamfara.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar jim kaɗan bayan komawar Matawalle APC a yau Talata.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun mai taimaka wa gwamnan na musamman kan harkokin watsa labarai Zailani Baffa, ta ambato Mai Mala na cewa: “Daga yanzu Matawalle ne jagoran jam’iyyarmu mai girma a jihar Zamfara.”

“Za ku saurari sauran shirye-shirye na samar da sabuwar jam’iyya daga wajensa nan gaba kaɗan,” in ji Buni.

A lokacin da yake karɓar tutar jam’iyyar, Gwamna Matawalle ya karɓi jagorancinta a yayin da ya ayyana kansa a matsayin mamba a cikinta.

Kazalika Gwamna Matawalle ya shiga jam’iyyar ne tare da dukkan sanatocin jihar da ke kan mulki a yanzu, da ƴan majalisar wakilan tarayya shida daga cikin bakwai da kuma dukkan ƴan majalisar dokokin jihar.

Da yake magana a wajen taron sauya sheƙar, tsohon gwaman Zamfara Abdulazeez Yari, ya ayyana goyon bayansa da kuma jajircewa don samun nasarar jam’iyyar, tare da addu’ar neman tsarin Allah daga duk wata masifa da za ta sake samun jam’iyyar.

Daga cikin waɗanda suka halarci bikin sauya shekaƙar har da gwamnonin Kano da Kaduna da Kebbi da Borno da Kogi da Neja da Yobe da Ogun da Katsina da Jigawa da kuma Filato.

Sannan tsohon gwamnan jihar Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ma ya halarta

62 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...