Siyasar Zamfara:Mu nai maka maraba da zuwa APC,Amma da Sharudda – Abdulaziz Yari

Date:

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara a ranar Litinin sun yi wani taro a jihar Kaduna inda suka tattauna kan sauya shekar da gwamnan jihar, Bello Matawalle ya yi zuwa jam’iyyar.


 Taron ya samu halartar tsoffin gwamnonin jihar Zamfara biyu, Abdulaziz Yari da Mahmud Shinkafi, da tsoffin sanatoci, ministoci da shugaban APC na jihar, Lawal M Liman.


 Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, tsohon Gwamnan, Abdulaziz Yari, wanda kuma shi ne jagoran APC a Zamfara, ya ce bayan tattaunawar da sukai, sun yanke shawarar tarbar Gwamna Bello Matawalle cikin jam’iyyar duk da turjewar da suka yi da farko, da sharadin zai ci gaba  bin ka’idojin jam’iyyar da akidunta na Samar da ci gaba.

 Ya ce duk da cewa Gwamna Matawalle ya gaza gudanar da shugabanci na Gari da hada kan daukacin mutanen jihar tun hawan sa mulki, APC a matsayin uwa Daya uba daya za ta ba shi damar zama a cikin jam’iyyar tare da fatan zai mutunta ka’idoji da Dokokin  jam’iyyar don cigaban al’ummar jihar Zamfara.


 A halin da ake ciki, Kwamitin Aiki na Jam’iyyar PDP ya rushe Kwamitin zartarwar ta a jihar Zamfara, tare da gargadin cewa gwamnan zai rasa kujerarsa bayan sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.


 Sakataren yada labaran na kasa, Kola Ologbondiyan, a wani taron manema labarai a ranar Litinin din nan ya bayyana hakan, ya kuma ce jam’iyyar za ta garzaya kotu don kalubalantar ficewar gwamnan daga jam’iyyar.

97 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Na sauke nauyin da Tinubu ya ɗora min – Gwamnan riko na jihar Rivers

Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas (Mai ritaya), wanda shi ne gwamnan...

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta Amince da kashe Naira Biliyan 18 don aiwatar da wasu aiyuka

  Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir...