Daga Halima Abubakar
Gwamnatin jihar Kano ta biya Naira Miliyan Dari 300 a Matsayin kasonta na Aikin Samar da Madatsar Ruwa a Garin Yan sabo dake Karamar Hukumar Tofa ta jihar Kano.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan Yayin Bikin biyan Kudin Diyya ga al’ummar da Aikin Zai shafi gonakinsu da Gidajen su da kuma bishiyoyinsu a Gidan gwamnatin Jihar Kano.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace Wannan Aikin da za’a gudanar Zai taimaka wajen inganta Rayuwar al’ummar yankin tare inganta harkokin Noma a jihar Kano da Kasa Baki daya.
Gwamna Ganduje yace gwamnatinsa tana baiwa harkokin Noma kulawar data dace domin bunkasa Rayuwar al’umma, Kuma yace Aikin Samar da aikin yi ga al’ummar yankin tare da Magance matsalar ambaliyar Ruwa ga al’ummar yankin.
Yace gwamnatin Jihar Kano zata biya Diyyar sama da Naira Miliyan 68 ga wadanda Suka chanchanta ,tare da bukatar suyi Aiki da Madatsar Ruwan yadda ya dace.
“Zamu yi iya Bakin kokarin mu wajen ganin an kammala Aikin akan lokaci Saboda Muhimmancin da Aikin yake dashi” Ganduje
Da yake nasa jawabin Kwamishinan Muhallin na jihar Kano Dr Kabir Ibrahim Getso yace Nan gaba kadan za’a gudanar da aiyukan zaizayar Kasa a Wasu Kananan Hukumomin Jihar Nan ta karkashin Hukumar yaki da Zaizayar Kasar da inganta Madatsun Ruwa ta Kasa.
“Za’a Aikin Magance Zaizayar Kasa a Unguwar Gayawa dake Karamar Hukumar Nasarawa d unguwar Tudun fulani dake Ungoggo dana Garin kamanda dake Kiru da dai Sauransu” Inji Dr Getso
A Jawabinsa Makaman Bichi Hakimin Tofa Alhaji Isyaku Umar Tofa yace idan an kammala Aikin Zai taimakawa al’ummar yankin Dama na Karamar Hukumar Tofa .
Wasu Daga Cikin al’ummar yankin sun bayyana Godiyarsu bisa Diyyar da aka basu da Kuma Aikin Madatsar Ruwan da za’a yi musu.
Aikin Samar da Madatsar Ruwan a Garin Yan sabo Aiki ne na Hadin Gwiwa tsakanin Gwamnatin tarayya da Bankin Duniya da Kuma Gudunmawar Gwamna jihar Kano.