Gwamnatin Jihar Kano Zata Dauki Likitoci 56 Aiki

Date:

Daga Halima A Musa


 Gwamnatin jihar Kano ta fara shirye-shiryen daukar Likitoci 56 a kokarin inganta bangaren lafiya a matakin farko a jihar nan.


 A jawabinsa yayin da yake yi wa masu neman aikin Likitancin karin haske yayin fara jarabawar gwaji da ka shiryawa Masu Neman aikin, Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kano Dokta Tijjani Hussain ya bukaci Masu Neman aikin dasu shirya domin fuskantar kalubalen da ke gabansu .
Cikin Wata sanarwa da Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar Maikudi Muhammad Marafa ya aikowa Kadaura24 yace Dr Hussain yana mai cewa idan Masu neman suka yi nasara za a horar da su a kan sha’anin jagoranci, Gudanar da Bayanai har ma da ayyukan Kula da Kiwon Lafiya a Matakin Farko.


 Sanarwar tace Dr Tijjani Hussain ya umarce su da su jajirce tare da sadaukar da kai lokacin da suka samu nasara a matsayin su na wadanda za su zama Ma’aikatan Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a matakin farko ta Jiha

56 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano Ta Karyata Rahoton Cibiyar Wale Soyinka Kan Take ‘Yancin ‘Yan Jarida

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahoton da...

Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Wadanda Za a Yi Wa Afuwa

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin a...

Majalisar Kano ta buƙaci a soke ɗaukar aikin kwastam da aka yi a kwanan nan

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga dukkan...

‎ ‎Kuskure ne Tinubu ya cigaba da ciyo wa Nigeria bashi bayan ya cire tallafin mai – Sarki Sanusi

‎ ‎ ‎Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN),...