Gwamna Ganduje yace ya kadu da Rasuwar Shekaran Gwammaja da Tijjani Sharubutu

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf


 Gwamnan jihar Kano, Dr.Abdullahi Umar Ganduje ya nuna alhininsa dangane da rasuwar dan jam’iyyar APCn nan Ahmed Abdullahi wanda aka fi sani da Shekaran Gwammaja wanda ya rasu a Ranar Talatar data gabata Sakamakon hadarin mota.


 Gwamnan wanda Mataimakinsa Dr.Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta yayin da yaje gidansu Mamacin domin Yi musu ta’aziyya a Gwammaja Quarters ya ce … ” Mun shiga cikin bakin ciki da muka samu labarin rasuwar Shekaran Gwammaja.”


 “Yana daga cikin Yan gwagwarmayar matasa masu hazaka wadanda suka dukufa wajen fadakar da jama’a a kafafen yada labarai game da manufofin jam’iyyar APC da kyawawan manufofi da shirye-shiryen Gwamnatin jihar Kano. Mutuwar sa babban rashi ne ga jihar Kano da kuma  APC, saboda irin gagarumar gudummawar da yake bayarwa ga rayuwar dan adam”. Ganduje ya bayyana


 Cikin Wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Mataimakin gwamnan Kano Hassan Musa Fagge ya aikowa Kadaura24 yace Gwamnan yayi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya baiwa iyalai Yan uwa da abokan Mamacin hakuri da juriya na Rashin Shekaran Gwammaja sannan kuma ya ba Jannatul Firdaus ga mamacin.


 Gwamnan ya kuma ziyarci unguwar Koki domin jajantawa dangin Alhaji Tijjani Sharubutu wanda ya rasu kwanan nan bayan fama da rashin lafiya.
 Duk da haka ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya jikansa da rahama ya bai wa iyalan juriyar rashin

290 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano Ta Karyata Rahoton Cibiyar Wale Soyinka Kan Take ‘Yancin ‘Yan Jarida

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahoton da...

Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Wadanda Za a Yi Wa Afuwa

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin a...

Majalisar Kano ta buƙaci a soke ɗaukar aikin kwastam da aka yi a kwanan nan

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga dukkan...

‎ ‎Kuskure ne Tinubu ya cigaba da ciyo wa Nigeria bashi bayan ya cire tallafin mai – Sarki Sanusi

‎ ‎ ‎Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN),...