Mazauna Wasu kauyuka a Zamfara sun kashe Yan Bindiga 10

Date:

Bayanai daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa wasu ‘yan fashin daji sun kwashi kashinsu a hannu a daren Juma’a lokacin da suke ƙoƙarin farmaki kan wasu ƙauyuka biyu da ke kusa da babban birnin jihar.

Ƴan fashin a kalla 10 ne suka mutu a cikin bata kashin da suka yi da ‘yan banga a ƙauyukan Kwaya da kuma Kura da ke ƙaramar hukumar Gusau.

Wannan na zuwa ne yayin da mazauna ƙauyukan nan shida da suka kai wa farmaki a shekaran jiya ke cewa adadin wadanda suka mutu yanzu ya kai 80.

A cewar mazauna yankin ‘yan fashin dajin sun gamu da gamon nasu ne a wani artabu da ‘yan banga a ƙauyukan Kwaya da kuma Kura lokacin da suka yi yunkuri afka musu da tsakar daren jiya.

Wani ɗan sa kai da aka yi fafatawar da shi, ya ce turjiyar da suka nuna da kuma ɗaukin da aka kai daga maƙwabtan ƙauyuka ne suka taimaka musu suka fatattaki maharan tare da hallaka 10 daga cikinsu.

Ya ce “Jiya da misalin sha biyu da ‘yan kai na dare, da yake ba barci muke ba muna gadi saboda halin da muke ciki. Sai ‘yan wancan garin suka kira mu suka ce mukai musu ɗauki ga ƴan fashin sun zo.

“Da haka muka je dauke da bindigoginmu na toka duk da cewa su suna dauke ne da AK47 amma a haka muka ci galaba a kansu har muka kashe mutum 10.

“Da suka ga haka sai suka gudu, ba su samu nasarar shiga garuruwan ba. Ko kaza ba su ɗauka,” a cewarsa.

Amma ya ce a yanzu suna buƙatar jami’an tsaro, “yanzu haka akwai mata da suka gudo daga ƙauyukan sun fi 3,000 don ƴan fashin sun ce sai sun dawo. don haka dole gwamnati ta taimaka ta turo mana tsaro.”

Mutumin ya ce gawarwakin ƴan fashin da suka kashe ɗin suna nan jibge bakin waɗannan ƙauyukan. “Na gansu da idanuna sosai.”

Wannan artabun ya zo ne yayin da mazauna ƙauyukan nan shidda na yankin Magami da suka fuskacin hare-hare ranar Laraba ke cewa har yanzu suna ci gaba da zaƙulo karin gawarwakin wadanda ‘yan fashin suka halaka daga daji.

Wata majiyar tsaro a jihar ta Zamfara dai ta tabbatar wa da BBC duka lamurran biyu, wato kashe ‘yan fashin daji 10 da kuma karuwar adadin wadanda suka mutu daga hare-haren na shekaran jiya zuwa tamanin.

Ita ma gwamnatin jihar ta Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin na Magami a cikin wata sanarwa, tare da yin Allah wadai da abin da ta kira tsabagen aikin ta’addaci kan bayin Allah da ke neman abin kai wa baka.

Sai dai ba ta ce komai ba kan adadin wadanda aka karkashen

149 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...