Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Tsohon gwamnan jihar kano Malam Ibrahim Shekarau, ya yabawa gwamnatin jihar kano ta jam’iyyar NNPP dake karkashin Jagorancin Abba Kabir Yusuf, Saboda kudaden da ta warewa Ilimi a kasafin kudin shekara mai zuwa.
” Babu shakka abin da suka yi abun a yaba ne saboda ni dai a Sani na babu wata gwamnati a kano da ta taba yin wannan hubbasar ta warewa harkar Ilimi kaso 30 cikin 100 na kasafin kudi”.

Kadaura24 ta rawaito Malam Shekarau ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da gidan talabijin na Rahama Tv dake kano.
” Kaso 30 cikin 100 na kasafi ba karamin hobbasa ba ne ko gwamnatin tarayya bata yi, abun da majalisar duniya ma ta bayyana kaso mafi karancin a kowacce gwamnati mai son cigaban Ilimi shi ne kaso 26 , to in har gwamnatin Kano ta bayar da kaso 30 cikin 100 to ya zama wajibi a yaba mata”. Inji Shekarau
Da dumi-dumi: Tinubu Ya Nada Mai Taimakawa Kan Al’amuran Nakasassu
Ya ce yana yiwa gwamnan fatan alkhairi, sannan ya yaba da kokarin da kwamishinan Ilimi Umar Haruna Doguwa yake yi wajen fito da ƙalubalen da yake fuskanta da Kuma yadda yadda yake ziyartar makarantu don ganin irin matsalolin da suke fuskanta.
Sanata Shekarau wanda shi ne Sardaunan kano ya kuma shawarci gwamnatin ta Abba Kabir Yusuf da kada ta nade hannu saboda ta yi wancan hubbasar , ta tashi tsaye don ganin ta cimma manufofin da ta sanya a gaba na inganta Ilimi a fadin jihar kano a tsahon wa’adin gwamnatin sa.