Zargin Bata Suna: Jaruma Hadiza Gabon ta Maka Wani a Kotu

Date:

Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu, wacce aka fi sani da Hadiza Gabon, ta maka wani Bala Musa, ma’aikacin gwamnati, a gaban wata kotun Majistare da ke zamanta a Titin Daura, a jihar Kaduna bisa zargin ɓata mata suna.

Jarumar, wacce ta shigar da ƙarar ta hannun lauyanta, Mubarak Sani, ta ce ta fuskanci munanan kalamai da kuma cin mutuncin daga jama’a saboda sharrin da wanda ake kara ya yi mata.

Ya kara da cewa, mutane musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo sun kira Gabon da macuciya, wacce ta riƙa cin kuɗaɗen Musa ta kuma ƙi auren sa, zargin da aka tabbatar da cewa karya ne.

Wanda ake tuhumar, ta bakin lauyansa, Naira Murtala, ya musanta zargin.

Rushe Filin Idi: Kotu ta Baiwa Gwamnatin Kano Sabon Umarni

Alkalin kotun, Shamsudeen Sulaiman, ya tambayi lauyan mai karar ko suna da shaidu, inda su ka amsa da cewa suna da su.

Alkalin kotun ya bayar da belin wanda ake kara da sharadin ya gabatar da wasu amintattun mutane biyu mazauna jihar Kaduna kuma dole ne su kasance ma’aikatan gwamnati.

Daily Nigeria ta rawaito Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba domin mai karar ya gabatar da shaidu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ƴan majalisar wakilai 2 na NNPP a Kano sun fice daga jam’iyyar zuwa APC

Wasu ‘yan majalisar wakilai biyu daga jihar Kano sun...

Wasu mutane na kokarin sayar da wata makaranta a Kano, al’ummar yankin sun nemi daukin gwamna Abba

Daga Rabi'u Usman   Al'ummar ya garin Bechi dake cikin karamar...

Gwamnatin Kano na duba yiwuwar hada kai da jami’ar Bayero don baiwa yan soshiyar midiya damar yin Difloma

Daga Isa Ahmad Getso   Gwamnatin Jihar Kano za ta duba...