Daga Abubakar Lawan Bichi
Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Nasir Ado Bayero Ofr yayi Kira da Yan jaridu da su rika bi ka’idojin aikin wajan gudanar da ayyukansu na Jarida.
Sarkin yayi kiran ne a fadarsa yayin da Shugaban Kungiyar Yan jaridu na Kasa reshe Jahar Kano Comr Abbas Ibrahim ya jagoranci tawar yan takarar kujera Sakataren Kungiyar Yan jaridu mata ta Kasa Wasila Ibrahim Ladan a fadarsa.

Alh Nasiru Ado Bayero yace Aikin Jarida aikin mai muhimmanci ga al’umma a matsayin dirka ta hudu a Gwamnati Damakaradiya, Sune suke sanar da jama’a ayyukan bangaren zartarwa da ayyukan majalisar da kuma bangaren Shari’a.
Zargin Bata Suna: Jaruma Hadiza Gabon ta Maka Wani a Kotu
Ya kuma yi fatan samun nasara ga yar takarar ta Sakataren Kungiyar mata yan jaridu ta Kasa Hajiya Wasila Ibrahim Ladan a kujera da take nema.

A Jawabinsa Shugaban Kungiyar Yan jaridu na kasa reshe jihar Kano Com. Abbas Ibrahim yace sunzo fadar Sarkin domin gabatar da Hajiya Wasila Ibrahim Ladan a matsayi yan takarar kujera Sakataren kungiyar mata yan jaridu tare da neman albarka Sarkin.
A wani cigaban Kuma Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Nasir Ado Bayero Ofr ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Funakaye dake Jahar Gombe Alh Yakubu Muhammad Kwairanga a fadar.
Sarkin na Funakaye yace yazo Fadar Sarkin ne domin jaddada zumunci wanda suka gada iyaye da kakani.
Haka zalika Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Nasir Ado Ofr ya karbi bakuncin Shugaban shiya ta banki Jaiz bank Hajiya Na’imatu Abdullah a fadarsa,
Alh Nasir Ado Bayero ya bawa yadda banki ke gudanar da ayyukansa a tsari addini masulunci abi a yabane, yayi Kira banki ya badada ayyukansa ako ina.