Ni ginshiki ne a PDP idan na bar ta mutuwa za ta yi– Kwankwaso

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa
 Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, yace yana da yakinin cewa jam’iyyar PDP za ta rushe da zar ya fita daga cikin jam’iyyar.
Kadaura24 ta rawaito Kwankwaso duk da cewa a halin yanzu baya jin dadin  jam’iyyar,Amma ya bada tabbacin har yanzu yana Cikin jam’iyyar Bai Kai ga fita ba.
 Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a wani shirin gidan Talabijin na Channels, a cikin shirin  Political Paradigm.
 Kwankwaso ya yi tsokaci kan wasu dalilan da suka bayan jin dadin yadda ake tafi da jam’iyyar PDP, inda ya ba da misali da abun da faru a taron shiyyar Arewa maso Yamma da aka yi kwanan nan a Kaduna.
 “Ya kamata in kasance daya daga cikin masu fada a ji a jam’iyya PDP,” Amma ana ganin ban Isa ba Kuma Wasu Suna raina matsayina a jam’iyyar wanda ni Kuma bazan lamunci irin wannan wulakancin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...