Jami’ar Baze da ke Abuja ta gudanar da bikin yaye ɗalibanta karo na 12, inda ta yaye rukunin farko na ɗaliban da suka yi digirin digirgir (PhD) tun bayan kafuwarta.
A yayin bikin, jami’ar ta ba da lambar girmamawa ga Shugaban ƙasar Senegal, Alhaji Bassirou Diomaye Faye, ta hanyar ba shi digirin girmamawa na “Doctor of Political Science (Honoris Causa)” saboda irin rawar da yake takawa wajen bunƙasa ilimi da dimokuraɗiyya a nahiyar Afirka.
Shugaba Faye, wanda jakadan ƙasarsa a Najeriya, Nicolas Auguste Nyouky, ya wakilta, ya nuna godiya bisa wannan karramawa, tare da yabawa Jami’ar Baze saboda jajircewarta wajen samar da ingantaccen ilimi da haɗin gwiwar ilimi tsakanin ƙasashe a nahiyar.

A jawabin ta na bikin yaye ɗalibai, Shugabar jami’ar ta bayyana cewa waɗanda suka kammala karatu sun zama jakadu na gari, wadanda suka nuna jajircewa da ɗa’a wajen cimma nasara. Ta taya su murna, tare da ƙarfafar su da su kasance masu amfanar da kansu da ƙasarsu da Ilimin da suka samu.
A bana, jami’ar ta yaye ɗalibai 972, ciki har da ɗalibai 647 da suka yi digiri na farko, sai dalibai 33 da su ka yi “Postgraduate Diploma”, sannan akwai dabibai 276 da suka yi “Master’s” da kuma 16 masu PhD wanda ke zama karo na farko da jami’ar ta yaye su.
Haka zalika, jami’ar ta sanya sunan Shugaban ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, Wanda shi ne Babban bako a yayin Bikin, a Makarantar yin Digiri. A cikin jawabin sa, Shugaba Bio ya yaba da yadda Jami’ar Baze ke ci gaba da haɓakawa da inganta ilimi da tarbiyya don samar da shugabanni masu hangen nesa a Afirka.
Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP
Jami’ar Baze ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi masu zaman kansu da ake mutuntawa a Najeriya, tana bayar da horo a fannoni da dama ciki har da injiniya, shari’a, kiwon lafiya, kimiyya, fasaha, da harkokin kasuwanci.
Shugabar jami’ar ta ce, jami’ar na da ma’aikata daga sassa daban-daban na ƙasar da ma ƙetare, tana da gogaggun masana daga masana’antu da fannin ilimi. Ta bayyana cewa, akwai Farfesoshi 14 a sashen shari’a, ciki har da Lauyoyi huɗu masu matsayin SAN, yayin da sashen Dangantakar Ƙasa da Ƙasa ke da jakadu uku da tsofaffin manyan hafsoshin soja da manyan sakatarori a gwamnatin tarayya.
Tun bayan kafuwarta, Jami’ar Baze ta yaye sama da ɗalibai 3,900 (baya ga waɗanda suka kammala a 2025), kuma a halin yanzu tana da ɗalibai fiye da 4,200. Jami’ar ta samu cikakkiyar shedar amincewa daga Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da sauran ƙungiyoyin ƙwararru ciki har da na Injiniya, Likitanci, Lauyoyi, da Gine-gine.
A ƙarshe, Shugabar jami’ar ta ce fitar da rukuni na farko na masu PhD ya nuna cika alkawarin jami’ar na samar da ingantaccen ilimi, bincike, da ɗalibai masu tarbiyya da hangen nesa, waɗanda za su taimaka wajen ci gaban ƙasa da duniya baki ɗaya.