Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Mai martaba sarkin gaya Alh Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya nada Malam Muhajid Bello Idris a matsayin sabon dagacin garin gumakka dake cikin karamar hukumar warawa.
Nadin nasa ya biyo bayan rasuwar mahaifinsa tsohon dagacin garin na gumakkan Mal bello Idris.
Sarkin Kano ya Jagoranci Sallar Jana’izar Matar Gwamnan Kano na farko
Mai martaba sarkin ya hori sabon dagacin da ya rike amanar al’umma da kuma sauraren koken su a koda yaushe .
Mun yi takaicin yadda muka rasa kujerar gwamnan kano – APC
“Muna horonka da ka guji shiga duk wata harka ta rashin gaskiya, sannan ka haɗa kai da sauran al’ummar ka wajen tabbatar da zaman lafiya da inganta Ilimin ‘ya’yan mu”. Inji Sarkin Gaya
Shi ma sabon dagacin garin gumakkan ya godewa Allah da ya nuna masa wannan Rana da Kuma Mai martaba sarkin na gaya
Ya kuma roki hadin kan al’ummar da zai jagoranta tare da rokon su da su taya shi da addu’o’in Allah ya kama masa.