Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta ƙara tsaurara matakan tsaro a yankunan da ake ganin suna fama da matsalar tsaro, a wani ɓangare na ƙoƙarin da ake ci gaba da yi na dakile hare-haren ‘yan bindiga da kuma dawo da zaman lafiya.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar aikowa Kadaura24.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya ziyarci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu domin sanar da shi halin da ake ciki game da matsalolin tsaro da suka shafi wasu sassan jihar Kano.

A cewar gwamnan, Shugaba Tinubu ya nuna damuwarsa kan lamarin, inda nan take ya bayar da umarnin turo wata tawagar jami’an tsaro ta musamman domin ƙarfafa aikin da ake yi a Kano.
Gwamnan ya kuma ce an fara shirye-shiryen ƙara ƙarfafa sufuri, kayan aiki da sauran tallafin da hukumomin tsaro ke bukata domin tunkarar hare-haren ‘yan bindiga .
Ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa kowane yanki na jihar ya sami cikakkiyar kariya.
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya sauyawa wasu kwamishinoni da ma’aikata gwamnati ma’aikatu
Haka kuma ya umarci jami’an tsaro da su ci gaba da mayar da hankali, su kasance masu saka idanu, tare da ƙara inganta tattara bayanan sirri cikin haɗin kai da al’umma.
Gwamna Yusuf ya ce bayanan da al’umma suke bayarwa na taka muhimmiyar rawa wajen gano barazana da kuma hana hare-hare tun kafin su faru.