Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatin sa na siyo jirage marasa matuka da kayan aiki na sa ido da saurin mayar da martani domin kare mazauna iyakokin Kano da Katsina daga hare-haren ’yan bindiga.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.

Wannan ya zo ne yayin da gwamnan ke duba shirin Joint Task Force (JTF) wajen tunkarar hare-haren kwanan nan a kananan hukumomin Tsanyawa da Shanono, inda aka sace mutane kimanin 5 a Tsanyawa da 10 a Shanono, ciki har da mace guda da ta rasa rayuwarta.
Matsalar tsaro: Tinubu ya turo tawagar Jami’an tsaro ta musamman Kano – Gwamna Abba
Gwamna ya roki mazauna yankunan da su ba da bayanai masu amfani kan motsin ’yan bindiga, sannan ya umarci JTF da su yi iyakar ƙoƙarinsu wajen kubutar da wadanda aka sace.
Ya tabbatar wa dakarun da iyalan da abin ya shafa cewa gwamnati na yin iyakar ƙoƙarin ta wajen mayar da wadanda aka sace ga iyalansu cikin kankanin lokaci.