Gwamnan Kano ya lambar yabon gwarzon gwamnan mafi aiyukan raya kasa a Nigeria

Date:

 

 

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da adalci, aiyukan more rayuwa da kyakkyawan shugabanci, a yayin taron shekara-shekara da kungiyar CREED ta shirya a Tropical Galeria, Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

InShot 20250309 102512486

Gwamnan, wanda Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya wakilta, ya yaba wa masu shirya taron bisa yadda suke ƙarfafa tattaunawa mai ma’ana kan tabbatar da doka, jagoranci da cigaban al’umma.

A jawabinsa, Gwamnan ya jaddada irin gyare-gyaren ta ɓangaren shari’a da gwamnatinsa ke aiwatarwa, musamman batun sake duba tsare-tsaren da suka daɗe a cibiyoyin gyaran hali, wanda ya bankaɗo matsalolin da suka haɗa da mutane da aka tsare na tsawon shekaru ba tare da shari’a, ko takardun shari’a ba, ko kuma ba tare da lauya ba.

Ya bayyana cewa an ɗauki matakan gaggawa don nemo takardun shari’a da suka ɓace, fitar da shawarwarin shari’a, tare da sakin wadanda bincike ya nuna ya kamata a sake su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...