Sanata Barau ya mayarwa da Gwamnatin Kano Martani

Date:

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya gargadi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya daina kokarin siyasantar da batun tsaro, ya mayar da hankali wajen warware matsalolin da Kano dake ciki.

Sanata Barau ya karyata zargin gwamnatin jihar cewa ya yi wasu kalamai da za su iya kawo tangarda ga tsaron jihar, yana mai kalubalantar gwamnati da ta nuna hujjar da take da ita akan ikirarin nata.

InShot 20250309 102512486

Ya ce matsalar tsaro ba ta bukatar rikici tsakanin bangarori, sai ma a nemi hadin kan masu ruwa da tsaki domin magance kalubalen matsalar tsaron da ke faruwa a wasu sassan Kano.

Sanatan ya kuma zargi gwamnatin jiha da rashin gudanar da mulki yadda ya kamata, yana mai cewa hakan ya janyo koma bayan ga Kano Sosai .

Gwamnatin Kano ta nemi a kama Ganduje da Barau

Ya bayyana wasu daga cikin gudummawar da ya ce ya bayar domin inganta tsaro, ciki har da ba da motocin sintiri, babura, gyaran ofisoshin ‘yan sanda da gina sabbin cibiyoyin horar da jami’an tsaro.

Sanarwar da mai taimakawa mataimakin shugaban majalisar dattawan kan harkokin yada labarai Isma’il Muddasir ya fitar, ta ce maimakon gwamnatin Kano ta zarge shi, ya kamata ta yi koyi da ayyukan da yake yi domin tsare rayuka da dukiyoyin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...