Ganduje Zai Kafa Hukumar Hisbah Mai Cin Gashin Kanta a Kano

Date:

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa yana shirin samar da hukumar Hisbah Mai zaman kanta a jihar Kano domin kawar da badala da yin umarni da kyakykyawan aiki.

Ya ce wannan ya biyo bayan korar wasu jami’an Hisbah fiye da 12,000 da gwamnatin Kano ta ta yi, inda yace kafa sabuwar hukumar Hisbah mai zaman kanta domin ci gaba da gudanar da aikace-aikacen addini da inganta tarbiyya zai taimakawa jami’an da sauran al’ummar jihar Kano .

InShot 20250309 102512486

Dr. Ganduje ya bayyana haka ne yayin karɓar rahoton kwamitin da ya kafa domin nazarin halin da jami’an da aka sallama suke ciki. Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da Hisbah Corps, Hisbah Marshal, da kuma Sashen Shawarwari.

“Wannan Hukumar Hisbah mai zaman kanta za ta kasance ƙarƙashin Ganduje Foundation,” in ji Dr. Ganduje.

Kwamitin dai wanda tsohon kwamandan Hisbah na Kano, Dr. Haruna Ibn Sina, ke jagoranta, ya haɗa da tsohon Manajan Daraktan KAROTA, Dr. Baffa Babba Dan Agundi, tare da wasu manyan malamai.

Rahoton ya ƙunshi cikakken bayani da shawarwari kan hanyoyin da za a bi domin farfaɗo da ayyukan waɗannan jami’ai tare da tabbatar musu da makoma mai dorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...