Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan Nigeria ‘Yan Aji na 33 a kwalejin horon soja ta National Defence College (NDC) a ranar Alhamis.
Da yake jawabi bayan karɓar rahoton, Tinubu ya ci alwashin yin nazari kan shawarwarin da suka bayar game da yadda za a shawo kan matsalar tsaron ƙasar.
“Dole ne mu ci gaba da gina Najeriya, kuma haƙƙinmu ne samar da mafita daga shawarwarin da kuka bayar,” in ji shi.

Shawarwarin nasu na zuwa ne daidai lokacin da ake fargaba da kuma tafka muhawara game da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump ta kutsawa Najeriya domin kare Kiristocin ƙasar bisa iƙirarin da ya yi – ba tare da hujja ba – cewa ana yi musu kisan gilla.
Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA
Kwamandan kwalejin, Rear Admiral Abdullahi Ahmed, ya ce Aji na 33 ya ƙunshi ɗalibai 99, ciki har da jami’ai 25 na sojan ƙasa, 16 daga sojan ruwa, 12 daga sojan sama, biyar daga rundunar ‘yansanda, 18 daga ma’aikatun gwamnati.