Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin Manjo-Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) a matsayinsa na shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) na wasu shekaru biyar.
Marwa, wanda aka fara nada wa mukamin a watan Janairun 2021 a zamanin Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi shekaru biyu a matsayin shugaban kwamitin ganin bayan ta’ammali da miyagun kwayoyi kafin a nada shi kan mukamin NDLEA.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Kasa Bayo Onanuga ya rabawa manema labarai a yau juma’a .

Sake nadin na nufin tsohon hafsan soja ɗan asalin jihar Adamawa zai ci gaba da jagorantar hukumar har zuwa shekarar 2031.
Buba Marwa, wanda ya taɓa zama gwamnan soja na jihohin Legas da Borno, ya yi karatu a Makarantar Soja ta Najeriya da kuma NDA.
Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance
Gabanin nadinsa, hukumar ta yi fice wajen gano miyagun kwayoyi, ciki har da cafke fiye da mutum 73,000 da ake zargi da safarar kwayoyi, da kama sama da tan miliyan 15 na miyagun kwayoyi daban-daban.
Haka kuma hukumar ta kaddamar da yunkurin wayar da kan al’umma kan illar shan miyagun kwayoyi a fadin kasar.
A cewar Shugaba Tinubu:
“Wannan sake nadin hujja ce ta gamsuwa da kokarin da ka yi na dakile safarar miyagun kwayoyi da kuma yaduwar su. Ina kira a gareka da cewa kada ka sassauta, musamman wajen bibiyar masu safarar kwayoyi da ke barazana ga rayuwar matasanmu.”