Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC a hukumance tare da abokinsa ɗan majalisar wakilai Rt. Hon. Sagir Koki, mai wakiltar Birnin Kano da kewaye.
A cewar Jibrin Kofa, an karɓe su hannu biyu-biyu a zauren majalisar wakilai daga manyan jami’an gwamnati da jam’iyyar APC. A wajen tarbar akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila; Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda; tsohon Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje; da kuma wasu fitattun jagororin jam’iyyar daga Kano da fadin ƙasar.

Jibrin ya bayyana godiya ta musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, da sauran ‘yan majalisa da sanatoci bisa kyakkyawar tarbar da suka yi musu. Ya ce za su ci gaba da aiki tare da sauran ‘yan jam’iyyar domin ci gaban ƙasa cikin jajircewa da sadaukarwa.
Idan za a iya tunawa Dan majalisar tun a ranar laraba ya tara magoya bayansa na kananan hukumomin kiru da Bebeji domin neman shawararsu kuma suka Amince a koma APC , wanda Kofa ya tabbatar da hakan a zauren majalisar wakilai ta Kasa.