Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu a kan kudirin dokar kafa Gaya Polytechnic, mataki da ya nuna jajircewar gwamnatinsa wajen faɗaɗa damar karatun gaba da sakandare mai inganci a fadin jihar.
Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Kadaura24 a ranar Juma’a.
Yace An gudanar da bikin sanya hannu a Fadar Gwamnatin Kano, inda Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, da Mataimakinsa, Rt. Hon. Muhammad Bello Butubutu, suka harta.

A yayin taron, Gwamna Abba, ya nuna farin cikinsa bisa yadda aka gudanar da dukkan matakan majalisa cikin kwanciyar hankali, tare da yabawa shugabancin majalisar bisa himmarsu wajen gina tsari mai ɗorewa ga bangaren ilimi a jihar.
Gwamnan ya ce kafa Gaya Polytechnic zai ba da sabbin damammaki ga matasa don koyon sana’o’i da fasahohin da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na farfaɗo da ilimi, ƙarfafa shi da kuma faɗaɗa damar koyo a matakai daban-daban, yana mai cewa sabuwar Makarantar fasahar muhimmiyar dama ce da za ta inganta rayuwar matasan jihar Kano.
Sanarwar ta ce kafa Gaya Polytechnic ya yi daidai da shirin gwamnatin jihar na samar da ilimi mai sauƙin samu ga kowane yanki, tare da ƙarfafa tattalin arzikin kananan hukumomi a sassan jihar.