Hankula sun koma zuwa ga Arewa yayin da matasa goma daga Arewacin Najeriya da suke shugabanci a harkokin kasuwanci suka samu gurbin karɓar lambar yabo ta CEO’s Network Africa Awards 2025, wacce ke yaba wa hazikan masu kirkira da shugabanni da masu kawo sauyi a nahiyar Afirka.
Za a gudanar da bikin bayar da lambar yabon a ranar 14 ga Disamba, 2025, a Harabar Majalisar Tarayya, Abuja, inda za a karrama mutune 140 daga cikin masu takara sama da 15,000 da aka gabatar daga sassan nahiyar – adadi mafi girma tun kafuwar shirin.
Daga cikin wadanda suka fito daga Arewa a bana akwai hadakar ’yan kasuwa da ’yan wasa da masu fasaha da masu fafutukar tallafawa al’umma da ke sake fasalta ma’anar jagoranci a Afirka ta zamani.

A rukuni na “Ɗan Kasuwa na Shekara”, sun hada da Aliyu Mohammed, Shugaban Kamfanin Sarkin Mota Cars; Al-Amin Muhammed Idris, Shugaban Interface Africa; da Fatima Babakura, wanda ta kafa Yerwa Secrets da Timabee. Waɗannan sunaye sun shahara wajen kirkire-kirkire da ci gaban kasuwanci da matasa ke jagoranta.
A rukuni na “Noma”, Aminu Nyako, Shugaban Sebore Group, yana wakiltar bangaren kasuwancin noma, inda yake fafutukar ganin an cimma isasshen abinci da ci gaba mai ɗorewa.
A “Waka da Nishaɗi”, fitaccen mawaki Joseph Justice Elsa, wanda aka fi sani da Firstklaz, yana ɗauke da tutar Arewa yayin da tasirinsa ke ƙaruwa a duniyar wakoki.
A bangaren “Siyasa da Gwamnati”, Sadiq Rabiu, Mataimaki ga Shugaban Ƙasa na Musamman kan Ci gaban Ƙwarewa, ya samu gurbi saboda gudunmawarsa wajen inganta matasa da sabbin dabarun manufofi.
A “Tasirin Jama’a”, matasa mata masu ƙwazo kamar Hassana Maina, Daraktar ASVIOL Support Initiative; da Asma’u Ribadu, Jami’ar Tasiri ta Yola Hub, suna samun yabo saboda aikin su wajen kawo canji da haɗa kan al’umma.
A “Wasanni da Lafiya”, Shawall Barau, Shugaban ƙungiyar kwallon kafa ta Barau FC, ya fito a fili saboda jagorancinsa wajen amfani da wasanni a matsayin hanya ta ƙarfafa matasa da ci gaban al’umma a fadin Najeriya.
Tare da taken “Driving Africa’s Resilient Reinvention” (Tukumar Sabon Ginshikin Dorewar Afirka), wannan kyauta ta 2025 na nufin haskaka sabon ƙarni na masu hangen nesa a nahiyar. Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban taron, idanu na mayar da hankali kan wadannan fitattun matasa goma daga Arewa – kuma tambayar da kowa ke yi ita ce: waye zai lashe kambin bana?