Majalisar Matasan Arewa (Northern Youth Assembly, wata ƙungiya da ke haɗa muryoyin matasa daga jihohi 19 na Arewa, ta bayyana takaicin ta kan yadda Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya nuna halayya ta rashin kamun kai da rashin mutunci ga wani ƙaramin jami’in soja a Abuja.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta aikowa Jaridar Kadaura24 mai dauke da sa hannun Shugaba Dr. Ali Muhammad da Sakataren Dr. Abdulhafiz Garba, Sakataren Janar.

Majalisarta ce abin da ya faru, wanda yanzu haka yake ta yawo a kafafen sada zumunta da jaridu, abin kunya ne da bai dace da matsayin minista ba. Majalisar ta bayyana cewa wannan lamari ya sake bayyana yadda Wike ke nuna girman kai, cin zarafin mukami da kuma raina mutuncin jama’a, maimakon ya zama abin koyi ga shugabanci nagari da hidimawa al’umma.
Majalisar ta ce, yadda Ministan ya wulakanta jami’in soja da ke kan aikinsa, abu da yayin ya sabuwa mutumtaka da dattako, sannan ya sabawa ƙa’idojin aikin gwamnati. Ta ce, hakan na nuna dabi’ar Ministan ta raina jama’a da kuma raina dubban matasa da ke kallon shugabanni a matsayin abin koyi.
Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano
A cewar ƙungiyar, irin wannan ɗabi’a ba ta dace da minista a cikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ba, wacce ke da manufar kawo sauyi da tabbatar da shugabanci mai adalci da kwarewa.
Majalisar ta ce a lokuta mabanbanta Ministan ya aika makamantan Irin wadancan laifuffukan da ake zargin Wike da aikatawa tun bayan da ya hau mukamin minista.
Saboda haka, ƙungiyar ta kira ga Shugaba Bola Ahmad Tinubu da ya sake nazari kan ci gaba da kasancewar Wike a matsayin Ministan Abuja, tare da yin la’akari da sauke shi daga mukami don nuna cewa gwamnati ba za ta yarda da cin zarafi da rashin mutunci ga jama’a ba.
“Najeriya tana bukatar shugabanni da za su karawa ƙungiyoyi kwarin gwiwa, ba waɗanda za su tozarta su ba. Tana bukatar shugabanni da za su zama abin koyi ga matasa, ba masu tsoratar da su ba,” in ji sanarwar.