Asibitin Kwararru na Best Choice ya sake bijiro da wasu ayyukan jin kai a wani bangare na cigaba da farantawa al’umma kamar yadda ya saba lokuta zuwa lokuta, duba da yadda Mai girma Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya jajircewa wajen tallafawa bangaren Lafiya a jihar.
Rahotanni sunce mahukuntan asibitin Best Choice zasu duba masu wadannan larurar kyauta, idan kuma abin ya kama za ayi aiki za’a biya kaso 50%, za kuma a fara ganin likitoci ne daga ranar Alhamis 13th ga Nuwamba 2025, zuwa Lahadi 16th ga Nuwamba 2025 kyauta.
Sanarwar tace wadanda aka tantance su kuma suke da bukatar ayi musu aiki, za a yi musu ragin kaso 50% cikin 100 kan yadda ake biya kafin wannan damar.

Za’a fara ganin marasa lafiyar ne tun daga ƙarfe 4 na yammacin Alhamis da sauran ranakun zuwa abinda ya sawwaka
Daga cikin jerin cututtukan da za a duba sun haɗar da
Cutukan Hanci, Kunne Da Makogaro
(Nose, Ear & Throat) akan ₦300,000 maimakon ₦600,000 kamar yadda ake biya a baya
Cire Kari (lipoma Excison) wato (Lipoma Removal) akan ₦100,000 maimakon 200,000
Aikin Kaba
Hernia Repair ₦200,000 maimakon 400,000.
Tiyatar Cire Gwuiwa wato Hydrocele Surgery akan ₦200,000 maimakon 400,000.
Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP
Tunda da farko da yake ganawa da Jaridar Alfijir labarai Shugaban asibitocin ƙwararru na Best Choice Kwamaret Auwal Lawal Muhammad. (Dan Malikin Garo) ya jaddada cewa suna gabatar da wadannan shirye shirye ne domin farantawa al’umma tare da rage musu radadi na halin da suka tsinci kansu ciki.
Lawal ya kuma sha alwashin cigaba da bujiro da sabbin shirye shirye na kula da kiwon lafiya da ayyukan jin kai ta hanyar amfani da hanyoyin zamani don yin gogayya da sauran na duniya.
Kar ku manta wannan dama ta dan wani lokaci ce, kar ku sake a baku labari, wanda yaji zai iya sanarwa da wanda bai jiba
Asibitin Kwararru Na Best Choice yana nan a mazauninsa na dindindin dake Plot 782/783 tal’udu kusa da makarantar Sheikh Bashir Eli Rayya
Hakazalika suna gudanar da ayyukan su ba dare ba rana tare da manyan kwararrun likitoci.

Za a iya tuntubar su ta yanar gizo bestchoiceclinic@gmail.com
Ko facebook Best Choice Specialist Hospital
Ko kira da whatsapp akan
+2347034951671
+234912 345 3534
+2342082443318
Mun zaɓi mu bada ire-iren waɗannan gudunmawar ne duba da yadda Mai girma Alh Abba Kabir Yusuf gwamnan jihar Kano yake bunkusa harkar Lfy da sauran muhimman bangarori domin saukakawa al-umma musamman masu karamin karfi a dukkannin fadin jihar