Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir Ibrahim Koki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.
A cikin wata wasikar da ya aikawa shugabar jam’iyyar ta mazabar Zaitawa , mai dauke da kwanan watan 11 ga Nuwamba, 2025, Sagir Koki ya ce ya yanke wannan shawara ne saboda rikicin cikin gida da ya dabaibaye jagorancin jam’iyyar a matakin ƙasa.

“Wannan rikici ya sanya da wuya in ci gaba da gudanar da aikina yadda ya kamata wajen wakiltar jama’ata na Kano Municipal a majalisar wakilai.” Inji Koki
Dan majalisar ya bayyana godiyarsa ga jam’iyyar NNPP bisa damar da ta ba shi ya wakilci jama’a a karkashinta, yana mai cewa gogewar da ya samu da kuma goyon bayan da aka nuna masa “sun kasance abin alfahari a gare shi hakan tasa dole ya gode mata.”
Ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da girmama shugabannin da mambobin jam’iyyar a kowane mataki.
Wasikar ta fara aiki daga ranar Talata, 11 ga Nuwamba, 2025.