Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Date:

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar Kano da safiyar ranar Litinin, inda ya sace wata motar Toyota Hilux kuma ya fita da ita ba tare da samun cikas ba.

Binciken DAILY NIGERIAN ya gano cewa barayin sun shiga gidan ne ta Kofa ta 4, inda suka yi dabara suka shiga harabar gidan gwamnati, suka kuma fice da motar misalin ƙarfe 5 na asuba.

Majiyoyi daga cikin gidan gwamnatin sun bayyana cewa bayan faruwar lamarin, an duba bidiyon CCTV, wanda ya nuna barayin sun fice ne ta babban ƙofar shiga da fita ta gidan gwamnati ba tare da wani ya tare su ba.

InShot 20250309 102512486

Rahoton ya nuna cewa Motar da aka sace na daga cikin ayarin motocin da ke yi wa mataimakin gwamnan Kano rakiya.

Wata majiya ta ƙara bayyana cewa sashin ofishin mataimakin gwamna ba ya samun tsaro, sai lokutan aiki ko kuma lokacin da mataimakin gwamnan yake ofis.

An rawaito cewa direban motar, Shafiu Sharp-Sharp, an tsare shi na ɗan lokaci domin yi masa tambayoyi kan lamarin.

Dambarwar Tantance Ramat a Shugabancin NERC: Barau Yana Kyashin Samar Da Wuta Don Farfado Da Kamfanoni Kano – Barista S S Umar

Majiyar ta ce: “Tuni an fara bincike. Ana ci gaba da tambayar direban yayin da Babban jami’in tsaron gidan gwamnatin wato CSO ke nazarin hotuna da bidiyon CCTV.”

Ta ƙara da cewa an riga an mika bayanan motar ga jami’an tsaro domin gano inda ta shiga da kuma kama wanda ya yi satar.

Duk kokarin da majiyar Kadaura24 ta yi na jin ta bakin mai magana da yawun Gwamna Abba Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, hakan ya ci tura domin bai amsa kira ko saƙon da aka tura masa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...