Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Date:

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ta sake tsayawa takarar wa’adi na biyu a shekarar 2027, tana mai cewa ya yi jagoranci na gaskiya da kawowa Kano cigaba a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Tukur Bala, ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai bayan kammala taron horaswa na kwanaki uku a Katsina. Ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ayyana dokar ta baci a fannin ilimi, matakin da ya haifar da ci gaba, ciki har da ɗaukar malamai kusan 9,000 da inganta walwalar su.

A cewarsa, gwamnatin ta kuma bai wa makarantun gwamnati kayan koyo da koyarwa, lamarin da ya taimaka wajen sa Kano ta zama ta farko a jarrabawar NECO ta 2025.

InShot 20250309 102512486

Tukur Bala ya ce Gwamna Yusuf ya gaji bashin yan fansho da ya kai sama da naira biliyan 46, amma yanzu haka ya riga ya biya fiye da biliyan 27. Ya kuma ce an samu gagarumin ci gaba a kokarin gwamnan na gyaran titunan dake birnin kano, inda yace yanzu haka duk inda ka zagaya ayyukan ake, tare da saka fitilun titi masu amfani da hasken rana domin inganta tsaro a jihar .

Ya bayyana cewa ayyukan samar da wutar lantarki na Tiga da Challawa-Goje na ci gaba da gudana, haka kuma an kammala tituna masu tsahon kilomita biyar Mafi yawan kananan hukumomi 44 da aka fara a zamanin Kwankwaso amma suka tsaya.

Ƙungiyar ta kuma yaba da kafa rundunar Neighborhood Watch da Rundunar yaƙi da masu kwacen waya. Bala ya ce gwamnati na bai wa mata 36,400 tallafin N50,000 a kowane wata, tare da tallafa wa matasa fiye da 5,000 da suka samu horo domin fara sana’o’i.

Inganta tsaro: Gwamnan Kano ba da kyauatar Motoci da babura ga Rundunar Hadin gwiwa

Ya ƙara da cewa an sabunta asibitoci 40 da wasu cibiyoyin kiwon lafiya a fadin jihar.

Ya ce la’akari da wadancan aiyukan da suka bayyana ya zama wajibi su goyi bayan gwamnan Abba Kabir sake neman kujerar a Karol na biyu domin cigaban da aiyukan alkhairin da ya faro.

“Za mara maka baya, ka sake tsayawa a takarar a shekarar 2027,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...