Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Date:

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY), ya yi kira ga ’yan Najeriya Musulmai da Kiristoci da su haɗa kai su yi addu’a kan barazanar da shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi na kai wa Najeriya hari bisa zargin kisan Kiristoci.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Kamal Yakubu Ali, ya aikowa Kadaura24, SKY ya bayyana cewa halin da ƙasar ke ciki na cike da barazana daga bangarori daban-daban, abin da ya sa wajibi a koma ga Allah tare da yawaita salati ga Annabi Muhammad (SAW) domin neman kariya da mafita.

Ya ce “Amurka da gwamnatin ta ba su isa komai ba idan mu ka roƙi Allah (SWT) domi shi ne mahaliccin Amurka da Najeriya, kuma shi kaɗai ne zai iya kare mu daga kowace irin barazana.”

InShot 20250309 102512486

SKY ya yi kira ga Musulmai su taru a masallatansu domin gudanar da addu’o’i na musamman, yana mai cewa wannan ba lokacin zargi ko rarrabuwar kai ba ne, lokaci ne na tuba, haɗin kai da yawaita addu’a.

Ya kuma shawarci gwamnati ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen shawo kan lamarin, domin tabbatar da zaman lafiya da mutuncin ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...