Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa ya fara harkokin siyasa tun kafin tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara taka rawa a manyan mukaman gwamnati.
Barau, wanda aka dade ana damawa da shi a siyasar Kano, ya ce ya shafe shekaru yana gudanar da ayyukan jam’iyya da fafutukar siyasa, a lokacin da Kwankwaso ke aiki a ma’aikatar ruwan sha ta jihar Kano. A cewarsa, hakan na nuna cewa ya riga tsohon gwamnan shiga fagen siyasa da dogon lokaci.

Sanata Barau ya bayyana haka ne yayin da yake karin haske kan tafiyar sa ta siyasa tun daga matakin matashi har zuwa matsayin da yake rike da shi a yau a majalisar dokoki ta tarayya.
Barau ya ce gogewar da ya tara tsawon shekaru ta taimaka masa wajen fahimtar yadda siyasa ke tafiya a Kano, musamman yadda dabi’u da tasirin ’yan siyasa ke sauyawa lokaci zuwa lokaci.
Masu sharhi kan siyasa sun ce furucin Barau na iya zama wani bangare na kokarinsa na fayyace irin rawar da ya taka a siyasar Kano tun kafin wasu fitattun sunaye su fara hawa manyan mukamai, tare da tunasar da irin yadda tarihi ya gina siyasar jihar zuwa matsayinta na yau.