Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Date:

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar sojin ƙasar ta gabatar wa shugaba Trump tsare- tsaren yadda za a kai wa Najeriya hari, bayan umarnin da shugaban ya ba wa shalkwatar tsaron ƙasar ta Pentagon bayan zargin ana kisan Kiristoci Najeriyar.

Jaridar New York Times ta bayyana cewa tsare-tsaren su ƙushi zaɓi uku na yadda sojojin Amurkan za su iya shiga Najeriya da suka haɗa da:

InShot 20250309 102512486

Gagarumin hari: wanda zai ƙunshi aika wata rundunar mayaƙan ruwa ta musamman zuwa gaɓar tekun Guinea tare da rakiyar manyan jiragen sama na yaƙi, waɗanda za su iya yin ɓarin wuta kan ƴanbindiga a yankin arewacin Najeriya.

Matsakaicin hari: wanda zai kunshi aika jirage marasa matuƙa, domin tattara bayanan sirri da ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin masu tayar da ƙayar baya, da ayarinsu da ababen hawansu.

Sassauƙan hari: wanda zai fi mayar da hankali ga batun samar da bayanan sirri, da bayar da taimakon kayan aiki, da kuma gudanar da sintirin haɗin gwiwa da dakarun Najeriya domin ganin an kakkaɓe ƴan ƙungiyar Boko Haram da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, kamar yadda jaridar ta wallafa.

Wannan dai na zuwa ne bayan barazanar da shugaban Amurkar Donald Trump, ya yi na kai hari Najeriyar saboda zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...