Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

Date:

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a jihar Kano sun shiga ruɗani bayan gano gawar wata tsohuwa mai shekaru 96, wadda aka tsinta a cikin ramin masai.

Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a.

A cewar sa, hukumar kashe gobara ta samu kira daga wani Usman Adamu, inda ya bayyana cewa wata tsohuwar ta faɗa cikin ramin masai a yankin.

InShot 20250309 102512486

“Mun karɓi kiran gaggawa da misalin ƙarfe 9:27 na safe a ranar Alhamis, 6 ga Nuwamba 2025, daga Usman Adamu, yabsanar da mu cewa wata mata ta fada cikin ramin masai a ƙauyen Sarai, Dawakin Kudu,” in ji sanarwar.

Da tawagar Jami’an hukumar suka isa wurin, sun gano cewa matar mai suna Habiba Ado, tsohuwa ce wadda take mai fama da tabin hankali”, kamar yadda ’yan uwanta suka bayyana.

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

An ce tun tsawon kwanaki hudu ’yan uwan ta ke neman ta Amma ba su ganta ba, sai dai daga bisani aka gano gawarta a cikin ramin.

’Yan uwan matar sun roƙi mai gidan da ya rufe ramin domin kauce faruwar irin wannan hatsarin a nan gaba.

Hukumar kashe gobara ta tabbatar da cewa an fito da gawar matar, sai dai an tabbatar da rasuwar tsohuwar tun kafin isowarsu.

An mika gawarta ga mai unguwa, Alhaji Musa Muhammad, domin yi mata jana’iza bisa ka’idar addinin Musulunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...