Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yaba wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa sukar da ya yi wa Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, saboda maganganun sa masu tayar da kura da ke barazanar yiwuwar kai harin soji a Najeriya.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana matsayar Kwankwaso a matsayin ta kishin ƙasa, yana kira ga sauran shugabannin jam’iyyun adawa su bar siyasa a gefe, su tsaya tsayin daka wajen kare martabar ƙasar nan a gaban abin da ya kira “ɗaukacin ƙalubalen waje.”

“Mun gode Sanata Kwankwaso saboda kishin ƙasa. Wannan lokaci ne da ya dace dukkan shugabannin siyasa, ba tare da la’akari da jam’iyya ba, su haɗa kai su tsaya wajen kare ƙasarmu a matsayin ‘yan ƙasa na gari,” in ji Onanuga.
Kwankwaso ya yi tsokaci kan barazanar da Trump ya yiwa Nigeria
Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya fitar da wata sanarwa inda ya yi gargaɗin cewa maganganun Trump na iya tayar da husuma ta addini da kuma ƙara ta’azzarar matsalar tsaro a ƙasar.
A shafinsa na X , tsohon gwamnan ya yi Allah wadai da matakin Trump na sake kiran Najeriya “ƙasa mai damuwa ta musamman” bisa zargin “kisan gillar da ake yi wa Kiristoci.”