Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, yana shirin ganawa da takwaransa na kasar Amurka, Donald Trump, domin tattauna batun zargin kisan kiyashi da ake cewa ana yi wa Kiristoci a Najeriya.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce ganawar za ta gudana ne a kwanaki masu zuwa”.
Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Nigeria
Bwala ya jaddada cewa shugabannin biyu sun tsaya tsayin daka wajen yaki da ta’addanci , yana mai cewa Trump ya daɗe yana goyon bayan Najeriya ta hanyar amincewa da sayar mata da makamai, wanda Shugaba Tinubu ya yi amfani da su sosai a yunkurin kawar da ta’addanci, lamarin da ya haifar da manyan nasarori.

“Shugaba Trump ya taimaka wa Najeriya matuƙa wajen amincewa a sayar mana da makamai, kuma Shugaba Tinubu ya yi amfani da damar yadda ya kamata wajen yaki da ta’addanci, kuma muna samun sakamako mai kyau,” in ji Bwala.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Trump ya ce Amurka za ta dakatar da duk wani tallafi da take bai wa Najeriya “idan gwamnatin Najeriya ta cigaba da bari ana kashe Kiristoci”.
Ya kara da cewa Amurka “na iya amfani da karfin soji domin kawo karshen ‘yan ta’addan da ke kashe Musulmi.