Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya buƙaci Amurka ta taimakawa Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci maimakon barazana.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi.

Kwankwaso yace “Na lura da yadda Shugaba Donald Trump ya nuna damuwa kan Najeriya. Yana da mahimmanci na jaddada cewa ƙasarmu ƙasa ce mai ‘yancin kai wadda mutanenta ke fuskantar barazana daban-daban. Rashin tsaron da muke fuskanta ba shi da alaƙa da addini, ƙabila, ko siyasa.”
Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Nigeria
“Ya kamata Amurka ta taimaki hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance waɗannan matsalolin, maimakon yin barazana da za ta iya ƙara raba ƙasarmu.”
Kwankwaso yace ya kamata gwamnatin Najeriya ta naɗa wakilai na musamman daga manyan jami’an diflomasiyyarta don shiga tsakani da gwamnatin Amurka.
Ya jaddada cewa ya zama dole a naɗa jakadu don wakiltar muradun Najeriya a fagen ƙasa da ƙasa.