Shugaban Kasar Amuruka Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soji a Najeriya, yana mai zargin gwamnatin kasar da kyalewa ana kashe kiristoci.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkaɓe abin da ya kira ƴanta’adda masu kishin Islama da ke aikata ta’asa.

Ya kuma yi barazanar dakatar da duk wani taimakon Amurka ga Najeriya.
Tuni Najeriya ta yi watsi da ikirarin cewa ana kashe kiristoci ba gaira ba dalili a yankin arewacin inda galibi musulmi suka fi yawa.
A bayanin da Mista Trump ya wallafa a kafar sadar zumuntarsa ta Truth a ranar Asabar ya ce ya ba ma’aikatar tsaron Amurka ta fara shirin ɗaukar mataki kan Najeriya – “Idan har gwamnatin Najeriya ta bari ana ci gaba da kashe musulmi,” in ji shi.