Zargin Kisan Kiristoci : Tinubu ya Karyata Shugaban Amuruka Donald Trump

Date:

 

Gwamnatin Najeriya ta yi martani kan jawabin shugaban Amurka Donald Trump kan zargin kashe kiristoci a Najeriya.

Trump ya ayyana Najeriya a cikin ƙasashen da “yake sa ido a kansu.”

Ya ce kiristanci na fuskantar babbar barazana a Najeriya,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke aikata wannan kisan gillar. “Saboda haka na ayyana Najeriya ƙasar da ake da damuwa a kanta.”

FB IMG 1753738820016
Talla

Bugu da ƙari, Trump ya ce ya bai wa ‘yanmajalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole umarnin fara bincike kan hakan kuma su kai masa rahoton sakamakonsa.

A martanin da ya mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta ce lamarin ba haka ba ne.

Wata Kungiya ta maka NBC da Arewa24 a kotu kan zargin karya ka’idojin yada shirye-shiryen Najeriya

A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ya ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar da ƙasashen duniya ke ba ta musamman kan batun haƙƙin ɗan’adam da haƙƙin addini, wannan batun na zargin kashe kiristoci a ƙasar ba haka ba ne. Duk ƴan Najeriya suna suna da ƴancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba.”

Sanarwar ta ce a ƙarƙashin mulkin Tinubu, gwamnatinsa na ƙoƙari sosai wajen yaƙi da ta’addanci da ƙarfafa gwiwa da kare rayuwar al’umma ba tare da nuna bambanci.

Gwamnatin ta ce Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka da ƙasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...