Wata kungiya mai zaman kanta, . Mai suna Islamic Research and Da’awa Foundation da ke Abuja, ta shigar da kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano kan Arewa24 TV da Hukumar Kula da gidajen Rediyo da Tv NBC, tana zargin gidan talabijin din da saba dokokin hukumar yada labarai na Nigeria.
Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne bayan korafe-korafen cewa wasu shirye-shiryen Arewa24 musamman “Mata A Yau” da “H-Hip Hop” na dauke da abubuwan da ba su dace ba Wanda kuma suka sabawa al’adun al’umma.

A wata wasika da ta aika zuwa ga Daraktan NBC shiyyar Kano, kungiyar ta nemi a fallasa duk wasu matakan da hukumar ta dauka kan korafe-korafen da aka yi kan tashar, bisa dokar Freedom of Information Act ta 2011.
Kungiyar ta ce an yi ta samun suka daga shugabannin al’umma da malamai, musamman kan zargin cewa wasu fitattun batutuwa a shirin Mata A Yau na karawa mata kwarin gwiwar “daukar doka a hannunsu” a kan mazajensu — al’amarin da suka ce ya saba da dabi’u da tsarin rayuwar Arewacin Nigeria .
Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu
Kungiyar ta hannun lauyanta Barr. Abba Hikima Fagge ya kuma zargi NBC da “gazawa wajen daukar mataki a fili” duk da yawan korafe-korafen da ake yi kan shirye-shiryen na tashar Arewa24.
Ta neman a cikin kwanaki bakwai, NBC ta bayyana irin rahotannin da ta karɓa kan shirye-shiryen Arewa24, binciken da ta gudanar, hukunci ko gargadin da ta taba yi wa tashar, da matsayin takardar tantancewar shirye-shiryen da ake zargi.
Kungiyar ta ce rashin amsa a cikin wa’adin doka zai zama karya dokar Freedom of Information Act, kuma zai iya zama hujjar daukar mataki na gaba a kotu.