Ra’ayin Isah Suleiman Ismail
31 Oktoba, 2025
A Yau juma’a, an soma yaɗa labarai cewa wai majalisar kansilolin Karamar Hukumar Bebeji ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar, Dr. Alhassan Salisu Bebeji. Wannan batu ya sa an tayar da jijiyoyin wuya, amma tambayar da ya kamata mu fara yi ita ce: A ina wannan dakatarwa ta samo asali ?
Gaskiya ita ce, doka ta bai wa kansiloli damar rubuta takardar neman a binciki ko a dauki mataki kan shugaban karamar hukuma, amma ba su da ikon su dakatar da shi kai tsaye. Dole ne su tura korafinsu zuwa majalisar dokoki ta jiha wacce ke da hurumin bincike da tabbatar da gaskiyar zargi, kafin a yanke hukunci.
Tambayar ita ce: Shin majalisar dokokin jihar kano ta karɓi korafin? Ta gudanar da bincike? Ta kira wanda ake zargi?.

Amsar ita ce: A’a. Saboda haka, ina kansilolin su ka samo ikon ayyana cewa wai sun dakatar da shugaban karamar hukumar ? Ya kamata su sani Doka ba ta ba su wannan hurumin ba.
Haka zalika, zaman da suka kira suna cewa tashinsa su ka yi a zauren majalisa, shin an yi shi ne bisa ka’ida? Shin akwai DPM ko CPO a wurin kamar yadda tsarin gudanar da zaman majalisa ke bukata?.
Amsar ita ma a’a ce. Ba a gudanar da wani zaman doka ba, kuma babu wani ma’aikacin gwamnati da ya tabbatar da hakan. Wannan ya sa al’amarin ya fi kama da taron gefen titi ko teburin mai shayi fiye da zaman majalisar doka.
Saboda haka, abin da kansilolin su ka yi ba wani abu ba ne illa katsalandan cikin hurumin da ba na su ba, kuma hakan na iya jawo musu matsala, domin majalisar dokokin jiha ba zata yi shiru a rika wuce gona da iri ba.
A tarihi ma, mutanen Bebeji ya kamata su tuna da irin wannan rikici da aka yi a zamanin Hon. Mudan Umar, lokacin da kansiloli 12 (banda na Gwarmai da Tariwa) su ka yi yunƙurin tsige shi amma abin yaci tura.
Haka ma a zamanin Ali Namadi, kansiloli 13 (banda na Gargai) su ka ayyana tsige shi amma abin ya ci tura, har ma aka dakatar musu da albashi saboda karya doka.
Saboda haka, wannan sabon rikicin ma bai sha bamban ba. Labarin dakatar da shugaban Bebeji tamkar wasan kwaikwayo ne kawai, ba wani abu da doka ta amince da shi ba.
Ku huta lafiya.
Wannan rubutun ra’ayin :
Isah Suleiman Ismail
31st October, 2025