Jami’ar Baze ta gudanar da gangamin wayar da kai kan lafiyar ƙwaƙwalwa

Date:

Jami’ar Baze da ke Abuja ta fara gudanar da bikin da ta saba yi duk shekara da ta yi wa laƙabi da Makon Cikar Burin Rayuwa na 2025, wanda ta fara a ranar Litinin, 7 ga Oktoba.

Taron, na tsawon kwanaki uku an shirya shi ne don wayar da kai kan lafiyar ƙwaƙwalwa da ci gaban burin rayuwa da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar ɗalibai.

Bikin ya sake jaddada matsayin jami’ar a matsayin gwarzuwa wajen kula da walwalar ɗalibai da ilimi a fannoni da dama.

An fara makon ne da tattaki , wanda aka yinwa laƙabi da Tattakin Lafiya (Health Walk) da Sashen Tallafin Ɗalibai ya shirya domin wayar da kan ma’aikata da ɗalibai kan muhimmancin lafiyar ƙwaƙwalwa.

Tattakin ya fara daga harabar jami’ar inda ta zagaya wurare masu muhimmanci kamar Body of Benchers, National Open University, Hedikwatar EFCC, da Kamfanin Optima Petroleum a Abuja.

Farfesa Adeniyi, Rijistaran jami’ar tare da Shugaban Tsaron Jami’a, ACP Greg F. Esele (mai ritaya), da Shugaban Sashen Tallafin Ɗalibai, ne su ka jagoranci tattakin, wanda ya samu gagarumar halarta daga ma’aikata da ɗalibai.

Wakili daga Sashen Kiwon Lafiyar Ƙwaƙwalwa na FMC ya yabawa Jami’ar Baze bisa wannan ƙoƙari, yana mai cewa wannan aiki ya zo a kan gaba daidai da yadda duniya ke gudanar da Ranar Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Duniya.

A rana ta biyu na makon, an gudanar da babban taro da ya haɗa manyan baki da masana.

Cikin waɗanda suka halarta akwai Ministan Harkokin Matasa, Comrade Olawande Emmanuel Ayodele; Mai ba Mataimakin Shugaban Ƙasa shawara kan Matasa da Mata, Hauwa Liman (wacce ta kasance babbar mai jawabi); Shugabar Jami’a, Farfesa Jamila Shu’ara; Mataimakin Shugaban Jami’a (Acad.), Farfesa Osita Agbu; da Rajista Farfesa Abiodun Adeniyi, tare da wakilai daga Ma’aikatar Kuɗi da FMC Jabi.

Taken taron na bana shine “Tasirin Matsin Tattalin Arziki Kan Lafiyar Ƙwaƙwalwa ga Matasa a Najeriya”, inda aka tattauna batutuwa da dama ciki har da: kariya ga ɗaliban da ke da buƙatu na musamman a harabar jami’a, yaki da shan miyagun ƙwayoyi da safararsu, fahimtar damfara a harkar saka jari da yadda za a kare shiga matasa cikin ayyukan kungiyoyin asiri da munanan dabi’u.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...