Nasarar da Ɗaliban Kano suka Samu a NECO Kokari ne na Gwamnatin Ganduje – Sanusi Kiru

Date:

Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Hon. Muhammad Sanusi Kiru, ya taya ɗaliban Kano murna bisa nasarar da suka samu a sakamakon jarrabawar kammala makaratun Sakandire ta NECO a Wannan Shekarar ta 2025, inda jihar ta zama ta farko a fannin Turanci da Lissafi.

Sanusi Kiru ya bayyana cewa wannan gagarumar nasara ba za a iya ta’allakata ga tasirin sauye-sauyen da gwamnatin Kano mai ci ba, sai dai alama ce dake nuna irin ingancceen fandisho da jarin da tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya zuba a bangaren Ilimi lokacin mulkinsa tun daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Kiru ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

A cewarsa, ingantaccen shirin da aka aiwatar a wancan lokaci wajen inganta makarantu, horas da malamai da kuma samar da kayan aiki shi ya gina tubalin da ɗaliban suka dogara da shi wajen cimma wannan matsayi.

Kano Ta Zama Zakara A Jarrabawa NECO Ta Bana

Kiru ya jaddada cewa ba adalci ba ne a jingina nasarar da aka samu kacokan ga gwamnatin mai ci a yanzu ba tare da tuna irin rawar da aka taka a baya ba. Ya ce irin waɗannan sakamakon manya ne daga tsare-tsare masu dogon zango da kuma jajircewar gwamnatin Ganduje wajen bunƙasa ilimi a Kano.

FB IMG 1753738820016
Talla

Ya kuma yaba wa ɗaliban, malamai, iyaye da dukkan masu ruwa da tsaki da suka bada gudummawarsu wajen ganin wannan nasara ta tabbata.

A cewarsa, ” mun kira ga gwamnati Mai ci da ta ƙara dagewa domin ci gaba da inganta harkar ilimi a jihar, domin amfanin al’umma nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...