Waiya da mutum 71 a Kano sun yi rantsuwar zama ya’yan cibiyar jami’an hulda da jama’a ta Nigeria NIPR

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

A ranar Alhamis ne Cibiyar Jami’an Hulda da Jama’a ta Kasa a Najeriya (NIPR) ta rantsar da sabbin mambobi 80 a jihar Kano.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida a jihar Kano kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya da sauran jami’an hulda da jama’a da masu aiki a wannan fanni sun yi rantsuwar zama mambobi na cibiyar NIPR ta kasa.

Cikin wannan adadi 80 da suka sha rantsuwar zama mambobin wannan cibiya 72 sun fito ne daga jihar Kano da uku daga Jigawa kana wasu biyar daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya da cibiyoyi masu zaman kansu.

FB IMG 1753738820016
Talla

Da yake jawabi a yayin bikin Kwamishina Waiya bayan taya murna ga wadanda aka rantsar ya sake jaddada muhimmancin gudanar da aiki bisa kwarewa da yin gaskiya da bin kai’doji yayin gudanar da ayyukan sadar da bayanai ga al’umma.

Ya ce gwamnatin Kano ta dukufa wajen ganin ana dabbaka aikin yada labarai da sadarwa cikin tsari da dattako.

A nasa tsokaci a wajen bikin rantsar da mambobin Farfesa Sule Ya’u Sule na sashin koyar da aikin jarida a Jami’ar Bayero ya ce da zarar an rantsar da wadannan mambobin za su ci gaba gudanar da ayyukansu bisa ka’idoji na wannan cibiya.

“Dole ne za ku dau rantsuwa ta kare martabar wannan aiki ku gudanar da aikinku bisa bin ka’idojin wannan cibiya za a baku wadannan ka’doji da za ku yi aiki a kansu.”

Tun da fari a sakonsa na maraba, mataimakin shugaban cibiyar Jami’an Hulda da Jama’a ta kasa NIPR Farfesa Emmanuel Dandaura, ya bayyana muhimmiyar rawa da aikin hulda da jama’a ke da shi wajen gina kasa.

Sai ya bukaci sabbin mambonin da su zamo masu darajawa da bin ka’ida da nuna kwarewa a yayin gudanar da ayyukansu.

Da yake gabatar da rantsuwar ga sabbin mambobin wannan cibiya shugaban Cibiyar ta NIPR Dr. Ike Neliaku yace wannan cibiya an samar da ita tun a 1963 kan ta samu tabbatuwa karkashin dokar soja mai lamba 16 a 1990.

IMG 20250802 WA0088(1)
Talla

Dr. Neliaku ya jaddada bukatar ci gaba da samun horo don gudanar da aiki cikin kima a aikin hulda da Jama’a.

Wannan biki na rantsuwar sabbin mambobin wannan cibiya dai ya zama aza damba gare su ta gudanar da aiki bisa bin ka’ida da sadar da bayanai masu tasiri a harkokin gwamnati da ayyukan al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...