Gwamnatin kano ta karbi rahoton kwamitin binciken yadda Namadi ya yi belin dilan kwaya

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta karbi rahoton kwamitin da gwamnan Kano ya dorawa Alhakin bincikar yadda akai  kwamishinan kula da harkokin sufuri na Jihar Kano Alhaji Ibrahim Namadi Dala ya yi belin Danwawu da ake zargi da hada-hadar kwayoyi.

FB IMG 1753738820016
Talla

Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya karbi rahoton kwamitin a madadin gwamnatin Kano.

Sakataren gwamnatin Kano yace kamar yadda gwamna Yusuf yake takatsantsan wajen daukar mutum aiki a kowanne mataki a gwamnati haka yanzu ma , idan an samu matsala da mutum sai an bi a hankali wajen daukar mataki domin yiwa kowanne bangare adalici, inda ya ce ba batu ne na gaggawa ba.

Gwamnatin Kano za ta maida gidan yarin da yayi shekaru 100 zuwa gidan tarihi

“Mun san cewa abin ya taba ran mutanan kano,kowa ya tofa albarkacin bakinsa ,mai kyau da akasin haka”,Inji Sakataren gwamnatin Kano

Ya tabbatar da cewa zai mika rahoton ga gwamna Abba Kabir Yusuf kuma nan gaba zai sanar da matsayin gwamnatin Kano akan lamarin.

A nasa jawabin shugaban kwamatin binciken da gwamna ya kafa, Barista Aminu Husaini ya ce sun tuntubi kowanne bangare kafin gabatar da rahoton.

Hukumomin da aka tuntuba a cewarsa sun hada da DSS da NDLEA da Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA da sauran masu ruwa da tsaki.

IMG 20250802 WA0088(1)
Talla

Haka kuma Barista Aminu ya ce, sun gayyaci shi kansa kwamishinan na sufuri domin ji daga gareshi, kuma ya bada hadin kai.

Haka zalika, kwamatin yace ya karbi dukannin takardun shari’a daga babbar kotun jihar Kano, domin yin nazari akansu.

Ya ce sun mika rahoton domin gwamna Yusuf ya dauki mataki na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...