Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dasa bishiyu miliyan 5 a jihar

Date:

Daga Ummakussum Sani Zubair

 

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a jiya Lahadi ya kaddamar da kamfen na dasa bishiyu miliyan biyar na 2025 a Dausayin Yanbawa da ke karamar hukumar Makoda.

Wannan shiri na da nufin magance illolin sauyin yanayi, inganta muhalli, da kuma ƙarfafa dorewar lafiyar muhalli.

FB IMG 1753738820016
Talla

Yayin kaddamarwar, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar samar da bishiyu a faɗin Jihar Kano domin inganta sauyin yanayi.

Ya bayyana cewa farfado da Dausayin, wanda aka yi watsi da shi tun bayan da aka kafa shi a 1972, wani bangare ne na dabarun inganta sauyin yanayi da bunkasa harkar noma na jihar Kano.

Gwamnatin kano ta karbi rahoton kwamitin binciken yadda Namadi ya yi belin dilan kwaya

Gwamnan ya kuma umarci rarraba irin bishiyar domin dasawa a ma’aikatu, da makarantu da masallatai da ma gidaje a daukacin kananan hukumomi 44 na jihar.

A nashi ɓangaren, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahir M. Hashim, ya baiyana cewa dashen bishiyun ya baiyana aniyar gwamnati ta farfado da muhallin Jihar da kuma inganta sauyin yanayi.

“Tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki daga gwamnati da kuma masu zaman kansu, za mu haɗa karfi da karfe da dukkan kananan hukumomi 44 domin dasa itatuwa da kiyaye su a makarantu, wuraren ibada, gidaje, gonaki da filayen al’umma.

IMG 20250802 WA0088(1)
Talla

Ina kira ga dukkan al’umma, cibiyoyi, da masu ruwa da tsaki da su ɗauki wannan kamfen a matsayin nasu.

Tare, za mu iya tabbatar da makoma mai cike da koren ganyaye da lafiya ga Jihar Kano,” in ji Kwamishinan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...