Suna Muhammad ya sake zama kan gaba a sunayen da ake raɗawa jarirai a England Wales

Date:

An fitar da sunayen jarirai da suka fi tashe a shekarar 2024 a Ingila da Wales, inda Athena da Yahya suka shiga cikin guda 100 na farko da aka fi sanya wa yara a karon farko.

BBC ta rawaito cewa Muhammad ya zama na ɗaya a ɓangaren maza, shekara biyu ke nan a jere, inda Noah da Oliver suka zo na biyu da na uku, kamar yadda yake a shekara ta 2023.

FB IMG 1753738820016
Talla

Olivia da Amelia ne sunayen yara mata na ɗaya da na biyu da aka fi sanyawa, karo na uku a jere, sai dai Isla ya fita daga cikin ukun farko a sunayen da aka fi sanya wa yara mata, inda Lily ya maye gurbinsa.

Ofishin ƙididdiga na Birtaniya ne ya fitar da alƙalumar, wanda shi ne ke tattara bayanan takardar rajistar haihuwa.

Sabbin sunayen yara mata da suka shiga 100 na farko su ne Eloise da Nora da Myla da Rosa da Athena da Sara da kuma Zoe.

Gwamnan Kano ya aikawa Majalisar dokoki sunan wanda zai shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawa

A ɓangaren maza kuma akwai Austin da Nathan da Vinnie da kuma Yahya.

Muhammad ya kare kambinsa na sunan da aka sanya wa jarirai maza ne inda aka sanya wa yara 5,721 sunan. Ya zamo sunan da aka sanya wa jarirai a yankuna biyar cikin tara na Ingila, sannan na 57 a Wales.

Haka nan sauran yadda ake rubuta sunan, kamar Mohammed, shi ne na 21 inda aka sa wa jarirai 1,760, sai kuma Mohammad a matsayin na 53, wanda aka sanya wa jarirai 986.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...