Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Date:

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Kasa na Kasafin Kuɗi, Hon. (Dr.) Abubakar Kabir Abubakar Bichi, ya biya kuɗin makaranta a karo na uku ga ɗalibai 121 ‘yan asalin ƙaramar hukumar Bichi da ke karatu a matakin digiri na biyu (Master’s) da digirin digirgir (PhD) a manyan jami’o’i daban-daban.

Kwamitin ilimi karkashin Hon. Abubakar Bichi, wanda Dr. Habibu Usman Abdu ke jagoranta, ne ya tantance waɗanda suka ci gajiyar tallafin, sannan aka raba kuɗin ga ɗaliban nan take kamar yadda ake yi a kowanne shekara.

InShot 20250309 102512486
Talla

Ga jerin jami’o’in da waɗanda suka ci gajiyar tallafin ke karatu:

Jami’ar Bayero (BUK) – 58

Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma – 24

Jami’ar Arewa maso Yamma (North West University), Kano – 08

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote – 07

Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria – 07

Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna – 04

Jami’ar Tarayya Dutse – 02

Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa – 02

Jami’ar Jos – 01

Jami’ar Najeriya, Nsukka – 01

Jami’ar Jihar Nasarawa, Keffi – 02

Makarantar Soji ta Najeriya (Nigerian Defence Academy), Kaduna – 02

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Hon. Abubakar Kabir Bichi ya shahara wajen nuna ƙwazo da ƙaunar ci gaban al’ummarsa ta Bichi da kuma Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya, musamman ta fuskar tallafin karatu, tsare-tsaren ilimi da sauran shirye-shirye.

Taron rabon tallafin kuɗin makarantar ya samu halartar wakilan jami’o’in da suka amfana, ma’aikatan ofishin ɗan majalisar, shugabannin al’umma, wakilan ƙungiyoyin ɗalibai da kuma jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...