Kwamitin Gawuna-Garo Ya Gudanar da Saukar Alƙur’ani da Addu’o’i na Musamman ga Dantata da wasu mutum 3

Date:

A ranar Asabar, 26 ga Yuli, 2025, Kwamitin Godiya da Bangajiya na Gawuna-Garo ya shirya wani babban taron saukar karatun Alƙur’ani mai girma da addu’o’i na musamman domin tunawa da addu’a ga marigayi Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata, marigayi tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dala, Hon. Mahmoud Sani Madakin Gini, marigayi tsohon shugaban ƙaramar hukumar Wudil, Hon. Abubakar Abdullahi Likita, da kuma marigayi Sheikh Malam Abdullahi Muhammad Yankaba, tare da sauran ‘yan uwa Musulmi da suka rigamu gidan gaskiya.

InShot 20250309 102512486
Talla

An gudanar da wannan taro ne a Masallacin da ke kallon gidan Mai Girma Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, a unguwar Miller Road, Bompai, Kano. Taron ya samu halartar al’ummar Musulmi daga sassa daban-daban na jihar Kano da ma wajenta, wadanda suka taru domin yin addu’a da roƙon rahamar Allah ga rayukan marigayun.

A cewar mai taimakawa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna kan harkokin yaɗa labarai, Abubakar Musa DK, “Taron ya kasance cike da natsuwa da zurfin ibada, inda malamai da dama suka gabatar da karatun Alƙur’ani da kuma gabatar da addu’o’in neman gafara da rahama ga marigayun.”

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin bincike kan kwamishinan da ya tsayawa wanda ake zargi da harkar kwayoyi

Ya ƙara da cewa, “Allah Ya gafarta musu, Ya kuma saka da alheri ga dukkan wadanda suka halarta da waɗanda suka yi fatan alheri a gare su. Amin.”

Taron ya kasance wani ɓangare na ci gaba da nuna godiya da tunawa da ayyukan alheri da gudunmawar da marigayun suka bayar ga al’umma kafin rasuwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...