Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya tsaya wa Suleiman Danwawu, ƙasurgumin dilan miyagun ƙwayoyi aka bada belin sa a kotu.
Kwamishinan ya kawo wa Danwawu ɗauki ne bayan da Mai Shari’a MS Shu’aibu, alƙalin da yai suna wajen tsauri a shari’a, ya sanya sharuɗɗan beli masu tsauri.
Bayan ya yanke hukuncin bada belin Wanda ake zargi a ranar 16 ga Yuli, DAILY NIGERIAN ta gano cewa alkalin ya umarci wanda ake zargi da gabatar da kwamishina mai-ci a Jihar Kano a matsayin wanda zai tsaya masa, tare da ajiye Naira miliyan biyar (₦5,000,000) a kotu.

Sai dai kuma abin da ake ganin da kamar wuya a samu kwamishina a gwamnatin Abba Kabir Yusuf da zai tsaya wa wanda ake zargin da laifin safarar miyagun ƙwayoyi, sai gashi Namadi ya bugi ƙirji ya rubuta takarda, yana bayyana kansa a matsayin Wanda sai tsaya wa Danwawu.
A wata takarda da ya rubuta a ranar 18 ga Yuli, 2025, kuma ya aikewa mataimakin babban rajistaran Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, Namadi ya nemi a amince ya tsaya wa Danwawu a bada belin sa.
Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Tinubu
DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, a ranar 21 ga Mayu, Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta shigar da ƙara akan Danwawu mai ɗauke da tuhume-tuhume guda takwas da suka shafi safarar ƙwayoyi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano.
Bayan gurfanar da shi a gaban kotu a ranar 28 ga Mayu, an dage sauraron buƙatar belin sa zuwa ranar 16 ga Yuni, sannan aka ajiye wanda ake zargin a gidan yari.
Ga takardar da ya rubutawa Kotun da kuma sauran bayanai

Daily Nigerian