Daga Hafsat Abdullahi Darmanawa
Kungiyar ma’akatan wucin gadi da suka gudanar da aikin zaben Kananan Hukumomin a Jihar sun bukaci Hukumar dake yaki da Cin hanci da rashawa ta Kasa ICPC da ta nisanta kanta da shiga harkokin siyasa cikin ayyukanta.
Shugaban kungiyar Auwal Shuaibu ya bayana hakan a wani taron manema labarai na gaggawa da Kungiyar ta shirya a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Auwal Shuaibu, yace sun isa Abuja ne bayan hukumar ta ICPC ta fitar da sanarwar gurfanar da Shugaban Hukumar Zaben Mai zaman Kanta ta Jihar Kano Farfesa Sani Lawan Malumfashi da Ma’aikatar hukumar guda biyu a gaban kotu a ranar Litinin 21 ga watan Yuni na 2025.
Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje
Kungiyar ta zargi wasu yan siyasa bangaran Yan adawa da kitsa lamarin domin bata sunan shugaban hukumar bayan yunkurin da suka yi ta yi wajen kawo cikan ga zaben da hakan bai tabbataba.
Kungiyar ta bayyana tsare-tsaren da KANSIEC ta gudanar a zaben na 2024 a matsayin wanda ya ke cike da adalci da gaskiya da hukumar ta biya ma’aikatan wucin gadin a bainar Jama’a domin tabbatar da an biya kowa hakkisa a hannunsa.
A karshe Kungiyar ta bukaci ICPC da ta yi duba na tsanaki wajen tabbatar da adalci tare da gujewa shiga harkokin siyasa cikin ayyukanta.