Daga Rahama Umar Kwaru
Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan takarar kujerar gwamnan Kano a jam’iyyar APC a zaben 2023 Alhaji Inuwa Ibrahim Waya ya ce ya je wajen gwamnan Kano domin tattauna batutwaun da suka shafi cigaban jihar Kano .
Kadaura24 ta rawaito Inuwa Waya ya bayyana hakan ne jiya juma’a a sahihin shafinsa na Facebook.

“Na kai ziyarar ban girma ga mai girma gwamnan jihar Kano Eng. Abba Kabir Yusif. Mun tattauna batutuwan da suka shaficigaban jihar kano”. Inji Waya
Tun bayan da hoton gwamnan Kano da Inuwa Waya ya fita ake ta yada jita-jitar cewa wayan Wai ya je gidan gwamnatin ne domin komawa Kwankwansiyya.